Shugaba Muhammadu Buhari zai gana da Donald Trump

Shugaba Muhammadu Buhari (daga hagu) da kuma Shugaba Donald Trump Hakkin mallakar hoto Reuters/Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari (daga hagu) da kuma Shugaba Donald Trump

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai zamo shugaba na farko daga nahiyar Afirka (Kudu da sahara) da Shugaba Donald Trump zai karbi bakunci a Washington.

Ana sa ran za su tattauna kan batutuwan tattalin arziki da tsaro da suka shafi kasashen biyu.

Sai dai wasu da dama za su zuba ido kan ganawar bayan da aka yi zargin cewa Mr Trump ya yi munanan kalamai kan kasashen Afirka.

Shugaba Trump ya musanta cewa yana nuna wariyar launin fata bayan da aka ba da rahoton kalaman nasa.

Me Buhari da Trump za su tattauna?

Wakilin BBC a Najeriya ya ce ana sa ran shugabannin biyu za su kawar da kansu daga waccan takaddamar domin mayar da hankali kan muhimman abubuwan da ke gaban kasashen nasu.

A gida, Shugaba Buhari na fuskantar matsalolin tsaro daban daban, ciki har da yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta shafe shekara tara tana tayar da kayar baya a Arewa maso Gabas da kuma rikicin kabilanci da kuma na makiyaya da manoma a wasu sassan kasar.

A don haka yaki da ta'addanci abu ne mai muhimmanci ga duka kasashen biyu.

Hakkin mallakar hoto Boko Haram
Image caption Tun shekarar 2009 Boko Haram ke tayar da kayar baya a Najeriya

Amurka ta sayarwa da Najeriya jiragen yaki 12 a kan kudi dala miliyan 496 domin taimaka mata a yakin da ta ke yi da Boko Haram.

A baya, tsohuwar gwamnatin Obama ta ki amincewa da cinikin jiragen, saboda zargin sojin Najeriya da take hakkin bil'adama, lamarin da suka sha musantawa.

A ganawar da za su yi a birnin Washington, Mr Trump da Shugaba Buhari za kuma su tattauna kan bunkasa dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Buhari, wanda ke neman wa'adi na biyu a 2019, ana hasashen zai bayyana cewa yana mai da hankali wurin bunkasa tsarin demokuradiyya duk da mummunan cin hanci da rashin ci gaba da ake fama da shi a kasar.

Bayan ganawa da Trump, ana sa ran shugaban na Najeriya zai gana da 'yan kasuwa da suka kware a fannin noma.

Sauran manyan jami'an gwamnatinsa kuma za su gana da shugabannin kamfanonin Amurka na fannin sufuri.

Wannan ne karo na biyu da shugabannin Amurka suke gayyatar Shugaba Buhari Fadar White House.

A shekarar 2015, tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya taba gayyatar shugaban na Najeriya zuwa Washington.