Donald Trump ya yaba wa Shugaba Muhammadu Buhari

Trump and Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Muhammadu Buhari ya zamo shugaba na farko daga nahiyar Afirka (Kudu da sahara) da ya gana da Mista Trump a Washington

Shugaban Amurka Donald Trump ya yaba wa takwaransa na Najeriya Muhammadu Buhari kan yadda yake yaki da ta'addanci a lokacin da suka gana a fadar White House.

Mr Trump ya ce Shugaba Buhari "ya jajirce" a yakin da kasarsa ke yi da ta'addanci kuma Amurka za ta ci gaba da aiki tare da Najeriya domin kawar da wannan matsala.

Sai dai ya ce "ana kashe Kiristoci a Najeriyar, inda ya ce za mu yi aiki kan hakan, domin shawo kan matsalar sosai da sosai, domin ba za mu bar hakan ya ci gaba da faruwa ba."

Shugabbannin sun kuma tattauna kan batutuwan tattalin arziki da kasuwanci da suka shafi kasashen biyu.

A nasa bangaren Shugaba Buhari ya yabawa rawar da Mr Trump ke takawa wurin samar da zaman lafiya a yankin Koriya, da kuma taimakawa Najeriya a yakin da ta ke yi da Boko Haram.

Sannan ya jinjina wa shugaban na Amurka kan yadda kasarsa ke tallafawa ayyukan jin kai a yankin Arewa maso Gabas.

Muhammadu Buhari ya zamo shugaba na farko daga nahiyar Afirka (Kudu da sahara) da ya gana da Mista Trump a Washington.

Kasuwanci

Kan batun kasuwanci, Mr Trump ya nemi Najeriya da ta bude kofofinta ga kamfanonin Amurka idan har tana son ayi kasuwanci da gaske musamman a fannin noma.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Trump na shugaba Muhammadu Buhari na gaisawa a fadar White House

Sai dai wannan lamari ne mai sarkakiya ganin yadda Najeriya ke kokarin bunkasa noma a cikin gida da kuma rage dogara ga man fetur.

Amurka da Najeriya na da alaka ta kut-da-kut wacce suka shafe shekara da shekaru suna martaba wa.

Cin hanci da rashawa

Mr Trump ya kuma yabi yadda Buhari ke yaki da ta'addanci, amma ya ce akwai cin hanci da yawa a kasar.

A don haka bai bayyana kai tsaye cewa ko Amurka za ta mayar da kudaden da ake zargin an sace daga Najeriya an boye a kasar ba.

Amma dai ya ce za su ci gaba da aiki tare da jami'an Najeriyar.

An zabi Shugaba Buhari ne bisa alkawarin yaki da cin hanci da rashawa a kasar da ta yi kaurin suna a wannan fage.

Ta'addanci da tsaro

A gida, Shugaba Buhari na fuskantar matsalolin tsaro daban daban, ciki har da yaki da kungiyar Boko Haram wacce ta shafe shekara tara tana tayar da kayar baya a Arewa maso Gabas da kuma rikicin kabilanci da kuma na makiyaya da manoma a wasu sassan kasar.

A don haka yaki da ta'addanci abu ne mai muhimmanci ga duka kasashen biyu.

Hakkin mallakar hoto Boko Haram
Image caption Tun shekarar 2009 Boko Haram ke tayar da kayar baya a Najeriya

Amurka ta sayarwa da Najeriya jiragen yaki 12 a kan kudi dala miliyan 496 domin taimaka mata a yakin da ta ke yi da Boko Haram.

A baya, tsohuwar gwamnatin Obama ta ki amincewa da cinikin jiragen, saboda zargin sojin Najeriya da take hakkin bil'adama, lamarin da suka sha musantawa.

A ganawar da suka yi a birnin Washington, Mr Trump da Shugaba Buhari sun tattauna kan bunkasa dangantakar tattalin arziki da ke tsakanin kasashen biyu.

Bayan ganawa da Trump, ana sa ran shugaban na Najeriya zai gana da 'yan kasuwa da suka kware a fannin noma.

Sauran manyan jami'an gwamnatinsa kuma za su gana da shugabannin kamfanonin Amurka na fannin sufuri.

Wannan ne karo na biyu da shugabannin Amurka suke gayyatar Shugaba Buhari Fadar White House.

A shekarar 2015, tsohon Shugaban Amurka Barack Obama ya taba gayyatar shugaban na Najeriya zuwa Washington.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Motar shugaba Muhammadu Buhari ta shigo cikin harabar White house
Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Muhammadu Buhari da shugaba Donald Trump na jawabi