Osinbajo ya yi Allah-wadai da harin masallacin Mubi

Harin Mubi Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Sama da mutum 30 ne suka mutu a harin yayin da wasu da dama suka mutu

Gwamnatin Najeriya ta umurci jami'an tsaron kasar da su tsaurara matakan tsaro a kasuwanni da sauran wuraren ibada a Mubi da ke jihar Adamawa.

Gwamnatin ta dauki matakin ne sakamakon wani harin kunar bakin wake da bam-bamai da aka kai wani masallaci da ke kasuwar garin Mubi.

Harin dai ya kashe akalla mutum 24 tare da jikkata wasu da dama.

Mataimakin shugaban kasar Farfesa Yemi Osinbajo ne ya bada umurnin.

Ya kuma umarci hukumar agajin gaggawa ta kasa wato NEMA ta gaggauta samar da magunguna da sauran kayayyakin agaji ga wadanda lamarin ya rutsa da su.

Wata sanarwa da kakakin mataimakin shugaban kasar Laolu Akande ya aikewa manema labaru ta ce, Farfesa Osinbajo ya kuma yi ta'aziyya ga iyalan wadanda suka mutu, sannan ya yi Allah-wadai da harin.

Osinbajo ya kuma nanata cewar jami'an tsaro na kokarin gano tare da hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aiki.

Kawo yanzu dai babu wata kungiyar da ta dau alhakin kai wannan harin.

Sai dai kungiyar Boko Haram ta sha kai hare-haren kunar bakin wake a arewa maso gabashin Najeriya ciki kuwa har da jihar ta Adamawa.