Kalaman Trump kan Najeriya na tada kura

Shugaba Trump da shugaba Muhammadu Buhari a fadar White House Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Trump da shugaba Muhammadu Buhari a fadar White House

Furucin da Shugaban Amurka Donald Trump ya yi cewa ba za su lamunci kisan da ake yi wa kiristoci a Najeriya ba sun jawo martani daga mabiya manyan addinan kasar biyu.

Kungiyar Kiristocin Najeriya wato CAN ta ce tayi maraba da kalaman da Shugaban ya yi lokacin ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari ranar Litini a fadar White House.

Sai dai wata kungiyar kare hakkin Musulmi a Najeriya wato MURIC ta yi watsi da kalaman inda ta ce wani kokari ne na bai wa kiristoci kwarin gwiwar yakar musulmi a kasar.

Shi dai shugaban Amurka, Donald Trump ya ce yana sha'awar zuwa Najeriya inda ya siffanta kasar a matsayin wata kasa mai ban mamaki.

Shugaban Amurka ya bayyana Najeriyar a matsayin kasar da cin-hanci da rashawa suka yi wa katutu amma ya ce gwamnatin Shugaba Buhari ta rage matsalar.

Muhammadu Buhari ya zamo shugaba na farko daga nahiyar Afirka (Kudu da Sahara) da ya gana da Mista Trump a Washington, inda suka tattauna kan abubuwan da suka shafi kasashen biyu.

Labarai masu alaka