'Donald Trump ya zama likitan kansa-da-kansa'

Harold Bornstein Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wasikar da Mr Bornstein ya sanya wa hannu ta bayyana Mr Trump a matsayin mai cikakkiyar lafiya

Kafafen yada labaran Amurka sun rawaito cewa tsohon likitan Shugaban kasar Donald Trump, ya ce ba shi ne ya rubuta wasikar da aka gabatar a shekarar 2015 kan cewa shugaban na da cikakkiyar lafiya ba.

Harold Bornstein ya shaida wa CNN cewa Mr Trump shi ne ya tsara yadda ya ke so a rubuta wasikar da kansa.

Har yanzu dai fadar gwamnatin Amurka ba ta ce komai ba a kan wannan batu.

Mr Bornstein, ya kuma ce mai tsaron lafiyar Mr Trump ya kai wani samame a ofishinsa a watan Fabrairun bara, inda ya kwashe duk wasu takardu da aka ajiye a kan batun lafiyar shugaban.

Likitan ya ce, wasikar da aka rubuta a 2015, da ta bayyana cewa Trump ya fi kowanne shugaban Amurka da aka taba zaba cikakkiyar lafiya, wanda ke cike da kuzari sosai, ba aikinsa ba ne.

Ya ce, Mr Trump shi ne ya rubuta duk abinda ya ke so wasikar ta kunsa, shi kuma ya yi hakan.

Abubuwan da wasikar ta kunsa

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Donald Trump bai ce komai ba game da wannan zargi kawo yanzu

Wasikar ta kunshi bayanan da ke cewa, Trump karfaffa ne kuma mai juriya, inda aka danganta hakan da cewa shi na daban ne.

Gwajin hawan jinin da aka yi masa da kuma sauran sakamakon gwaje-gwajen da aka yi masa, sun birge sosai saboda lafiyar da aka nuna yana da ita.

Kazalika a cikin wasikar, an rubuta cewa Mr Trump, ba shi da wani alamun ciwon daji wato kansa ko kuma wata alama da ke nuna cewa an yi masa aiki a gabobinsa.

Karin bayani a kan wasikar

Makonni kafin a gabatar da wasikar, Mr Trump ya rubuta a shafinsa na twitter cewa, bayanin lafiyata da Mr Bornstein zai gabatar zai nuna cewa lafiyata kalau.

Mr Trump wanda ya kasance shi ne shugaban Amurka na farko mafi tsufa da aka zaba a tarihin kasar, ya kuma rubuta a shafinsa na Facebook cewa:

"Na yi matukar sa'a da na ke da kwayoyin halitta masu kyau".

A watan Janairun 2018, an shafe sa'oi uku ana bincikar lafiyar Mr trump, saboda jita-jitar da ake yadawa a kan matsalar tabin hankali da yake da ita.