Wurare hudu da Buhari da Trump ke kamanceceniya da juna?

Shugaba Trump da shugaba Buhari Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Donald Trump da Muhammadu Buhari suna da kamanceceniya ta wurare da dama

Yayin da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ke ziyara a Amurka, BBC ta dubi abubuwa hudu da shugaban da mai masaukinsa Donald Trump suka yi kamanceceniya da juna.

Donald Trump ne dai ya gayyaci shugaban na Najeriya zuwa Washington ne domin su tattauna kan abubuwan da suka shafi kasashen nasu.

Muhammadu Buhari ne ya zamo shugaban Afirka (Kudu da Sahara) na farko da Mr Trump ya gayyata fadar White House.

To ko wadanan abubuwa ne suka hada shugabannin biyu?

1) Sun hau mulki suna da shekaru fiye da 70

Shekarar Shugaba Buhari 73 lokacin da ya yi mulki a shekarar 2015.

Shi kuwa Mr Trump shekararsa 70 lokacin da ya zama shugaban kasa a bara.

2) Zabensu ya ba kowa mamaki

Shugaba Muhammadu Buhari shi ne dan hammaya na farko da ya yi nasara a zaben shugaban kasa a tarihin siyasar Najeriya.

Ya samu galaba a kan Shugaba Goodluck Jonathan - ba a taba samun shugaban kasa mai ci da ya sha kaye a tarihin kasar ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shugaba Donald Trump lokacin da yake maraba da Shugaba Muhammadu Buhari a fadar White House

A Amurka kuma, Hillary Clinton wadda aka rika hasashen cewa ita ce za ta yi nasara.

Amma kwatsam sai Trump, wanda hamshakin dan kasuwa kuma dan takarar jam'iyyar Republican, ya yi nasara bayan da wasu jihohi da jam'iyyar Democrat ta ke mulki suka zabe shi.

3) Akwai sabani tsakaninsu da 'yan jarida

Shugaba Trump ba ya boye rashin gamsuwarsa da 'yan jarida da kuma sauran kafofin watsa labarai.

Shugaba Buhari wanda tsohon shugaban gwamnatin soji ne, bai cika sakin jiki da 'yan jarida ba musamman na cikin gida, yana bayyana manufofin gwamnatinsa ne a duk lokacin da ya yi tafiya zuwa kasashen waje.

Kuma shi ma ya sha samun sabani tsakaninsa da 'yan jarida ko kafafen sada zumunta, inda yake zargin cewa an yi wa kalamansa mummunar fahimta.

4) An san su da yin katobara

Shugaba Trump mai barota ne a sakonnin da ya ke tura wa a shafinsa na Twitter kuma ana zarginsa da kiran kasashen Afirka wulakanttatu, ko da yake ya musanta zargin da ake yi masa a kan cewa ya nuna wariyar launin fata.

Shi ma Shugaba Buhari ya fuskanci lamura irin wadannan.

Ya taba maida martani ga kalaman da matarsa ta yi inda ya ce aikinta kawai ta dafa masa abinci kuma a baya-baya nan ya fusata matasan Najeriya inda ya ce suna jiran gwamnati ta samar musu da komai kyau.


Bayani kan Shugaba Muhammadu Buhari a takaice:

Hakkin mallakar hoto Photoshot
Image caption Wata mai goyon bayan Buhari na sumbatar hotonsa da aka manna
  • Shekararsa 72
  • An zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 28 ga Maris 2015
  • Ya yi shugaban mulkin sojan Najeriya daga 1984 zuwa 1985
  • An hambare shi a juyin mulki
  • Ya samu shaidar rashin kare hakkin dan adam
  • An yi amanna ba shi da cin hanci da rashawa
  • Mai ladabtarwa ne - a kan sa ma'aikatan gwamnati tsallen kwado idan suka yi lattin zuwa aiki
  • Musulmi ne daga arewacin Najeriya
  • Ya tsallake rijiya da baya a wani hari da Boko Haram ta kai masa