Mahaukaciyar guguwa ta hallaka mutum 100 a Indiya

Guguwar da ta afkawa yankin Bikaner Hakkin mallakar hoto PTI
Image caption Guguwar ta shafi ungwanni uku da ke jihar Rajasthan da kuma wasu sassa na jihar Uttar Pradesh

Akalla mutum 95 ne suka hallaka yayin da wasu da dama suka jikkata lokacin da mahaukaciyar guguwa mai dauke da kasa ta afkawa jihohin Uttar Pradesh da Rajasthan a arewacin Indiya.

Guguwar ta lalata turakun wutar lantarki da bishiyoyi da gidaje da kuma dabbobi a ranar Laraba.

Da dama daga cikin wadanda suka rasa rayukansu na barci ne lokacin da gidajensu suka rufta bayan da tsawa mai karfin gaske ta afkawa gidajen.

Mahaucikaciyar guguwar mai dauke da kasa, aba ce da aka saba gani a wasu sassan Indiya a lokacin zafi amma ba a taba samun asarar rayuka irin wannan ba .

Mutum 64 suka hallaka a jihar Uttar Pradesh, 43 daga cikinsu a lardin Agra inda a nan ne fittacen ginin nan na Taj Mahal yake.

Jami'ai sun ce watakila adadin ya karu.

Bishiyoyi da bangon da suka fado sun kashe mutane da dama a jihar.

Gwamnan jihar Yogi Adityanath ya umurci jami'ai a kan su tabbatar sun sa ido kan aikin rarraba kayan jin kai.

Kwamishinan aikin jin kai na jihar Sanjay Kumar ya fadawa Kamfanin Dillancin Labarai na Indiya PTI cewa gwamnatin jihar "ta nemi a samar mata da cikakken rahoto dangane da abinda ya faru a wuraren da matsalar ta fi kamari".

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Daruruwan turakun wutar lantarki sun fado a wasu garuruwa da ke jihohin biyu
Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Bishiyoyi da suka fada da kuma bangon da suka ruguje sun kashe mutane da dama a jhohin biyu
Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Da dama daga cikin wadanda suka mutu suna barci ne lokacin da gidajensu suka ruguje

Mahaukaciyar guguwar ta kuma shafi wasu yankuna da suka hada da Rajasthan da Alwar da Bharatpur da Dholpur inda mutum 31 suka hallaka.

Jami'ai sun ce guguwar ta yi barna sosai a yankin Alwar .

An dai rufe makarantun da ke yankin.

Gwamnatin jihar ta kuma yi shelar biyan diyyar rupee 400,000 kwatankwacin dala 4,400 ga iyalan mamatan.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Wannan mutumin na cikin mutane da dama da aka ceto daga cikin gidjensu a Agra

Labarai masu alaka