Anil Kapoor zai aurar da 'yarsa Sonam Kapoor

Sonam Kapoor da angonta Anand Ahuja Hakkin mallakar hoto Bollywood News
Image caption Sonam Kapoor da angonta Anand Ahuja, wanda dan kasuwa ne

Jaruma Sonam Kapoor za ta amarce inda za ta auri saurayinta Anand Ahuja da aka jima ana ta yada jita-jitar soyayyarsu.

Za a yi wannan aure ne a ranar 8 ga watan Mayun 2018, wani kayataccen biki irin na Punjabi a Mumbai.

Mahaifin Sonam Kapoor wato Anil Kapoor, wanda shi ma jarumi ne, shi ne ya sanar wa da manema labarai ranar auren na 'yarsa

Rahotanni sun bayyana cewa, tuni Sunita Kapoor mahaifiyar Sonam ta fara shirye-shiryen bikin, inda ta fara da gyaran gidanta da ke Juhu da za a yi taron bikin.

'Yan uwa da abokan arziki dai na ta zumudin ganin wannan ranar biki, haka ma magoya bayan amarya Sonam, sun zaku da zuwan ranar.

Za a fara wannan kasaitaccen biki ne a ranar Litinin 7 ga watan Mayun inda za a fara da sakun lallai da suke cewa 'Mehindi.'

Sannan a washegari ne za a daura aure da safe, kafin da yamma kuma a yi shagali kamar yadda aka rubuta a katin bikin.

Mahaifin amarya Anil Kapoor, na daga cikin wadanda za su yi rawa a wajen bikin inda zai yi rawa da wakar fina-finansa kamar 'My name is Lakhan''

Haka shi ma dan uwan Sonam Kapoor wato Arjun Kapoor wanda da ne a wajen yayan uban amarya, shi ma zai cashe a wajen bikin.

Hakkin mallakar hoto E TIMES
Image caption Katin bikin auren Sonam Kapoor

Jarumi Ranveer Singh na daga cikin wadanda za su nishadantar da mahalarta biki.

Haka kuma Jahnvi Kapoor da suke 'ya'yan wa da kani da amaryar, kuma 'ya a wajen marigayiya Sridevi Kapoor, ita ma za ta cashe a wajen bikin, ind za ta kwaikwayi waka da rawar da mahaifiyarta ta yi a cikin wasu daga cikin fina-finanta.

Wacece Soonam Kapoor?

Hakkin mallakar hoto Getty Images
  • Sonam Kapoor ta fara fitowa a fina-finan Indiya a shekarar 2005
  • Fim dinta na farko 'Saawariya' wanda ta fito da Ranvir Kapoor.
  • An haife ta a ranar 9 ga watan Yunin 1985 a Chempur da ke Mumbai.
  • 'Yar jarumi Anil Kapoor ce da Sunita Kapoor.
  • Ta yi digirinta ne a Singapore inda ta karanci wasan kwaikwayo irin na dabe, (theatre and arts)
  • Tana daga cikin jarumai matan da tauraruwarsu ke haskawa a yanzu.
  • Wasu fina-finanta sun hada da 'I Hate Luv Storys' da 'Aisha da Mausam' da 'Players da Prem Ratan Dhan Payo' da kuma 'Khoobsurat'.

Tarihin soyayyar Sonam da mjinta Anand

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Sonam Kapoor da mahaifinta Anil Kapoor

A watan Mayun 2015 aka fara rade-radin cewa 'yar fim Sonam Kapoor ta fara soyayya da Anand Ahuja.

Anand shi ne mai kamfanin hada kayan kawa na Bhane, kuma shi ne ya fara bude shagon takalman sneaker mai suna VegNonVeg.

Da alama ta burge shi wajen iya sa kaya, domin dukkansu masoya kayan kawa ne.

Tun wancan lokacin ne Sonam da Anand suka rika jan hankulan mutane.

Bayan wata sanarwa da iyalan Kapoor da na Ahuja suka fitar cewa Sonam da Anand za a daura aurensu ranar 8 ga watan Mayu, dukkan rade-radi game da soyayyarsu a watannin da suka gabata ya kawo karshe.

Ana sa ran jarumai maza da mata, da suka yi tashe a shekarun baya da na yanzu za su halarci wajen bikin.

Labarai masu alaka