Mutumin da ya lakume Big Mac 30,000 cikin shekaru 46

Don Gorske wanda ya lakume Burger na Big Mac 30,000 a cikin shekaru 46 Hakkin mallakar hoto Not Specified
Image caption Don Gorske wanda ya lakume Burger na Big Mac 30,000 a cikin shekaru 46

Kalacin Big Mac nau'in abinci da ake kira sandwich, wanda kwanannan ya cika shekara 50 da kamfanin MacDonalds ya fara sayar da shi.

Amma ba wannan ne kawai dalilin da kalacin na Big Mac ya kafa tarihi ba, domin akwai wani mutumin Amurka da kawo yanzu yaci Big Mac din har dubu talatin.

Shekaru hamsin kenan da aka fara sayar da burgern Big Mac a gidajen abinci na McDonalds a sassan duniya daban-daban.

Amma a jihar Wisconsin ta Amurka akwai wani mutum da yafi kowa kaunar burgern na Big Mac.

Wannan mutumin shi ne Don Gorske - wani tsohon ma'aikacin gidan yari - wanda kuma shi ke rike da kambun wanda yafi kowa cin burger na Big Mac a duniya kuma tuni sunansa ya shiga littafin nan na Guiness Book of World Records.

A yanzu, shekarunsa 46 kenan da fara cin Big Mac, kuma ya ci na 30,000. Na san za a yi mamaki, amma lallai ya ci Big Mac har 30,000 a cikin shekaru 46!

Don Gorkse ya ce babu abincin da ya fi kauna kamar burger na Big Mac:

"Burgern dadi gare shi, a gareni jin sa nake kamar Cakula, shi yasa bai taba ginsa ta ba tun da na fara cinsa, kuma har yanzu shi ne kalacin sandwich da na fi kauna a duniya."

Don ya ce a cikin shekaru 46, kwanaki takwas ne kawai ya tsallake bai ci Big Mac ba - wadanda suka hada da lokacin da yake tafiye-tafiye, da ranar da mahaifiyarsa ta mutu, da kuma ranar da dusar kankara mai yawa ta sa aka rufe dukkan shagunan garinsu, har da na McDonalds. Shi yasa yanzu ba ya sakaci - ya kan ajiye burgern na Big Mac a firji don kaucewa bacin rana.

A shekarun da suka gabata, Don ya lakume kusan ton uku na naman sa, kimanin shanu goma kenan, kuma ya kan rubuta komai a cikin wani littafi domin maganin mantuwa. Amma abu mafi ban mamaki shi ne cewa duk da yawan naman da yake ci, amma ba shi da matsalar hawan jini samsam.

A yanzu yace yana kokarin ganin ya kafa sabon tarihi - na cin Big Mac da suka kai 40,000 - tarihin da Don yace zai kafa nan da shekaru 14 masu zuwa.

Labarai masu alaka