DJ Cuppy: Arzikin mahaifina ya sa dole na yi aiki

DJ Cuppy Hakkin mallakar hoto Getty Images

Fitacciyar mai kula da saka wakoki a wajen biki, Florence Ifeoluwa Otedola, wadda aka fi sani da suna DJ Cuppy, ta ce arzikin mahaifinta, na sa ta ta zage dantse wajen aiki.

Mahaifinta, Femi Otedola, daya ne daga cikin attajiran da suka fi kudi a Najeriya.

DJ Cuppy, wadda 'yar Najeriya ce mai saka waka, ta sanar da BBC cewar kasancewa 'yar mai hali bai sa ta zauna ba tare da wani aikin yi ba.

Florence Ifeoluwa Otedola, wadda ake cewa DJ Cupcake a baya saboda yadda take son kek, 'ya ce ga hamshakin dan kasuwar mai, Femi Otedola.

Wakilin BBC, Alan Kasujja, ya nuna mata cewar ai ba sai ta yi wani aiki sosai ba tun da dai tana da kudi.

Amma ta ce mahaifinta ne yake ba ta kwarin gwiwar yin aiki:

"Na ga bai taba zama cewa komi ya ishe shi ba, har yanzu yana tashi da misalin karfe biyar na safe".

"Ina jin wannan ya sa ina son in nemi na kaina."

Labarai masu alaka