NAFDAC ta rufe kamfononin hada kodin uku

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Kalli bidiyon yadda matasa ke rububin shan kodin

Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC) ta rufe kamfanoni uku masu hada maganin tari na kodin.

Hukumar ta ce ta yi hakan ne domin ta samu ta gudanar da bincike kan zargin da ake yi wa kamfanoni na sayar da maganin kodin ba bisa ka'ida ba.

Jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abubakar Jimoh, ya shaida wa BBC cewa hukumar ta dauki wannan matakin ne saboda kamfanonin basu ba su hadin kai yadda ya kamata ba.

An ambato sunayen kamafanonin da hukumar ta dakatar a cikin rahoto na musamman da BBC ta yi kan yadda kodin ke fitowa daga kamfanoni zuwa masu shan kwaya ba bisa ka'ida ba.

Kamfanonin hada magungunan sun hada da Emzor da Bioraj da kuma Peace Standard.

Kawo yanzu kamfanonin ba su komai ba kan wannan samamen, amma wani jami'i a Bioraj ya tabbatarwa da BBC cewa an rufe kamfanin nasu.

A baya dai kamfanonin sun musanta daurewa masu safarar kodin gindi da kuma dillancinsa ba bisa ka'ida ba kamar yadda rahoton BBC ya gano suna yi.

Maganin Kodin - yadda girman matsalar ta ke

  • Kodin magani ne da ke rage zafin ciwo ko na jiki amma yana cikin magungunan da ke sa maye.
  • Idan aka sha shi fiye da kima, to yana janyo tabin hankali kuma yana yin illa ga koda ko hanta ko zuciyar mutum
  • An fi hada maganin tari na kodin da lemun kwalba kuma dalibai ne suka fi shansa.
  • Daga kasashen waje ne ake shigowa da kodin, amma a cikin Na jeriya ne kamfanoni fiye da 20 suke hada magani
  • Hukumar yaki da miyagun kwayoyi ta kasar na kokarin kawarda da matsalar.
  • A samamen da taka kai a baya-baya nan, ta kwato kwalaben Kodin 24,000 daga cikin wata babbar mota a jihar Katsina.
  • Ta'ammali da kodin babbar matsala ce a Afirka, inda ake samun rahotanni game da wadanda ba su iya rabuwa da shi a Kenya da Ghana da Niger da kuma Chadi
  • A shekarar 2016, gwamnatin Indiya ta hana amfani da shi a kasar sakamakon rahoton da ta samu game da yawan masu ta'ammali da shi a matsayin kayan maye

Labarai masu alaka