Ina tsoron mutuwar Zakzaky a hannun gwamnati - Campbell

Sheik Ibrahim Elzakzaky Hakkin mallakar hoto IMN
Image caption Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya dade yana saka kafar-wando daya daga gwamnati a Najeriya

Tsohon Jakadan Amurka a Najeriya, John Campbell, ya ce idan har Najeriya ta ci gaba da tsare shugaban kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta Shi'a (IMN) to za a iya samun rikici irin na Boko Haram.

Mr Campbell, wanda mamba ne a majalisar huldar jakandancin Amurka, ya ce idan Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya mutu a hannun gwamnati to "komai zai iya faruwa a kasar".

Sama da shekara biyu kenan gwamnatin Muhammadu Buhari na tsare da Sheikh Zakzaky da matarsa a wani kebabban wuri da ba a bayyana ba, duk da cewa kotuna da dama sun bayar da belinsa.

A watan da ya wuce ne gwamnatin jihar Kaduna ta tuhumi malamin tare da wasu mutum uku da laifuka takwas ciki har da kisan wani soja a shekarra 2015, lamarin da suka sha musantawa.

Sojan mai mukamin kofaral na cikin ayarin da ke tare da Hafsan Sojin kasa Janarar Tukur Burutai lokacin da suka yi arrangama da 'yan shia a garin Zaria a ranar 12 ga watan Disamba na shekarar 2015.

Daga bisani kuma sojoji sun kai wa jagoran 'yan Shi'a hari a gidansa da ke Zaria inda suka kashe mutum sama da 300.

Sai dai magoya bayan malamin sun ce mutanen da aka kashe musu sun doshi 1,000, sannan aka yi awangaba da wasu da dama.

Tsohon Jakada Campbell ya ce 'yan Shi'a a Najeriya "sun yi kama da Boko Haram ta fuskar kafa gwamnati".

"Mun ga yadda gwamnatin kasar Iran ta nuna rashin jin dadinta lokacin da aka kama Zakzaky. Ba mu sani ba ko kasar na tallafawa 'yan Shi'ar Najeriya da kudade" in ji shi.

Mun san yana tsare ne a hannun gwamnatin tarayya.

Ya kara da cewa "gwamnatin na cewa ba za ta sake shi ba har sai gwamnatin jihar da ya sabawa ta yanke shawara, wato kenan gwamnatin jiha ce take tuhumar El-Zakzaky ba ta tarayya ba".

Me zai faru idan ya mutu a hannun gwamnati?

Hakkin mallakar hoto WhatsApp
Image caption 'Yan Shi'a na ci gaba da zanga-zangar neman a sako jagoransu

Mr Cambell ya bayanna wasu abubuwa biyu da ya nemi gwamnatin Najeriya ta aiwatar domin shawo kan matsalar tun kafin ta gagari kundila.

Abu na farko shi ne gwamnatin Najeriya ta tabbatar Zakzaky da matarsa sun sami kulawar likitoci sosai saboda idan ya mutu a hannun gwamnati, "to babu wanda zai iya cewa ga abun da zai biyo baya".

Masanin diflomasiyyar ya ce abu na biyu shi ne gwamantin tarayya ta ja hankalin gwamnatin jihar Kaduna da ta bayar da belin Zakzaky, sai kuma a jira a ga abun da shari'a za ta yi.

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayanna kungiyar ta IMN a matsayin haramtaciyya kuma ta hanata gudanar da taruka.

A farkon watan da ya gabata ne magoya bayan Sheikh Zakzaky suka fara zanga-zanga cikin lumana a kowace rana inda suka nemi a sako mu su jagoran nasu.

Sai dai sun sha ruwan hayaki mai sa hawaye daga jami'an tsaro wadanda suka zarge su da ta tada fitina, zargin da suka musanta.

Labarai masu alaka