Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran

Donald Trump Hakkin mallakar hoto EPA

Shugaban Amurka ya janye daga yarjejeniyar da Amurka ta kulla da Iran da sauran kasashen duniya domin kawo karshen shirin nukiliyar kasar ta Iran.

Mr Trump ya kuma sanar da cewa za a kakabawa Iran sabbin takunkumi kuma duk kasar da ta ci gaba da mara mata baya za ta dandana kudarta.

Ya kara da cewa ba a dauki matakan da suka dace ba wurin sa ido kan yarjejeniyar, a don haka ba ta aiki yadda ya kamata.

Mr Trump ya dade yana bayyana adawarsa da yarjejeniyar wacce aka kulla a 2015, wacce a karkashinta Iran za ta takaita shirinta na sarrafa makamashin nukiliya domin a rage mata takunkumi.

Shugabannin kasashen Turai na kallon shirin a matsayin hanyar da ta fi dacewa wurin hana Iran mallakar makaman nukiliya, kuma wakilansu sun gana da na Iran a ranar Talata ba tare da Amurka ba.

Anasa bangaren Shugaban Iran Hassan Rouhani ya yi gargadin cewa Amurka za ta yi da-na-sanin ficewa daga jarjejeniyar.

Ya ce Iran za ta shiga cikin matsala ta wani dan lokaci ne kawai amma daga bisani komai zai koma daidai.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi wa Iran alkawarin rage mata takunlkumi a karkashin yarjejeniyar

A karkashin yarjejeniyar dai Iran za ta takaita aikinta na inganta makamashin nukiliya domin kasashen duniya su rage mata takunkumin da aka sanya mata.

A yanzu hankali zai karkata ne kan martanin da Iran za ta mayar da kuma mataki na gaba da sauran kasashen da ke goyon bayan jarjejeniyar za su dauka.

Tuni dai kasashen Birtaniya, Faransa, Rasha, Jamus da China suka nuna aniyarsu ta cigaba da aiki da yarjejeniyar, wacce aka sanya wa hannu a lokacin tsohon Shugaba Barack Obama.

Trump dai ya yi korafin cewa yarjejeniyar ta takaita shirin nukiliyar Iran ne kawai na wani kayyadadden lokaci, sannan ba ta hanata mallakar makamai masu linzami ba.

Shugabannin Turai sun yi kokarin shawo kansa ta hanyar kai ziyara Amurka a 'yan kwanakin nan.

Sai dai rahotanni sun nuna cewa sun amince a kan ba su yi nasarar shawo shugaban ba.