'An sake samu bullar cutar Ebola a Congo'

Ebola ta lakume rayuka da dama a yammacin Afirka Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Har yanzu a na cigaba da binciken rigakafin Ebola

Jamhuriyar Dimokradiyar Congo ta ce an samu barkewar annobar Ebola a kasar, da kawo yanzu ta haddasa mutuwar mutane da dama.

Ma'aikatar kiwon lafiyar kasar ta ce mutum 17 sun mutu a garin Bikoro da ke arewa maso yammacin kasar, kuma gwaje-gwajen da aka aiwatar na nuna cewa biyu daga cikinsu Ebola ce ta kashesu.

Kafin sanar da bular Cutar, jami'an kiwon lafiya a yankin sun ce sun samu mutum 21 da ke fama da zazzabin da ke janyo zub da jini.

Hukumar lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce tawagar kwararu na kan hanyar zuwa yankin.

Wannan dai shi ne karo na 9 da ake samu bullar Ebola a Congo tun shekara ta 1967.

Cutar Ebola dai ta kashe fiye da mutum dubu 11 a yammacin Afrika a shekarar 2014.

Labarai masu alaka