Najeriya: Mace ta 'kashe' mijinta da maganin bera a Kano

Jami'an Hisbah na sunturi a birnin Kano a ranar 29 ga Oktoba, 2013. Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Hukumar Hizbah mai kula da dokokin shari'ar Musulunci na kokarin wayar da kan iyaye domin su daina yi wa 'ya'yansu auren dole

Hukumomi a jihar Kano ta Najeriya sun tuhumi wata mata 'yar shekara 16 da laifin kashe mijinta, Auwalu Isah, ta hanyar ba shi maganin bera.

Dan sanda mai gabatar da kara, Aluta Mijinyawa, ya ce matar da ke zama a kauyen Shittar da ke Karamar Hukumar Danbatta ta aikata aika-aikar ne a ranar 22 ga watan Afrilu.

Mijinyawa ya ce matar da dafa wa mijin nata abinci ne da maganin bera, inda ya ci kuma ya mutu jim kadan bayan hakan.

Matar, wacce ba a bayyana sunanta ba, ta musanta tuhumar da ake yi mata.

Bayanai sun nuna cewa an aura mata mutumin ne ba tare da tana sonsa ba, kuma ana ganin hakan ne ya sa ta dauki wannan mataki da ake zarginta da shi.

Dan sandan ya sanar da babbar kotun majistire ta Kano wani mutum ne a kauyen ya sanar da 'yan sanda lamarain kwana guda bayan afkuwar hakan.

Mai Shari'a Fatima Adamu ta babbar kotun majitiren Kano ta bada umarnin a ajiye wadda ake zargin a gidan wakafin yara.

Sannan ta dage saurarar karar zuwa ranar 7 ga watan Yuni.

Sai dai wakilin BBC a Kano ya ce akwai yiwuwar a dauke shari'ar daga wannan kotun saboda ba ta da hurumin saurarar karar.

Batun auren dole da kuma matsalolin da kan taso a sakamakonsa sun dade suna faruwa a sassan Najeriya da dama.

A shekara ta 2014 ma na gurfanar da wata matashiya Wasila Umar, 'yar shekara 14, a gaban kotu bayan da ta amince cewa ta sanya wa mijin da aka tilasta mata ta aura maganin bera a binci, inda ta kashe shi.

Sai dai daga bisani kotu ta yi watsi da tuhumar kamar yadda gwamnatin jihar ta nema, tana mai cewa wacce ake zargi yarinya ce da aka yi mata auren dole.

Hukumar Hizbah mai kula da dokokin shari'ar Musulunci na kokarin wayar da kan iyaye domin su daina yi wa 'ya'yansu auren dole.

Labarai masu alaka