Rooney zai koma Amurka da wasa

Wayne Rooney Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Wayne Rooney ya koma Everton daga Manchester United a watan Julin 2017

Wayne Rooney ya amince ya bar Everton domin taka-leda a kulob din DC United na Amurka kan fan miliyan 12 da rabi.

Rahotanni sun ce wakilan Rooney tuni suka isa Amurka domin tattauna sharuddan yarjejeniyar.

Tsohon Kaftin din na Ingila kuma ya nuna a shirye yake ya bar Everton.

Zuwa yanzu dai babu wani cikakken bayani game da yarjejeniyar.

Rooney ya koma Everton ne a watan Yulin 2017 daga Manchester United.

Sai dai kuma yanzu babu tabbas daga bangaren kocin Everton Sam Allardyce kan makomar Rooney a kulub din.

Rooney ya shafe shekaru 13 a Manchester United bayan ya baro Everton tun yana shekara 18.

Ya lashe kofin Premier biyar da kofin Zakarun Turai, kuma Rooney ne ya fi yawan cin kwallo a raga a Manchester United.

Wasu rahotanni sun ce Rooney ya amince ya koma DC United har zuwa 2020. Amma sai a watan Yuli ne za a bude kasuwar musayar 'yan wasa a Amurka.

A kwanan nan ne kocin Everton Sam Allardyce ya yi watsi da rahotannin da suka ce Rooney zai bar Kulub din saboda ba ya jin dadin aiki da shi.

Rooney dai ya buga wa Everton wasa 31 a kakar bana, inda ya ci kwallo 11 a matsayin wanda ya fi yawan cin kwallaye a kulub din a bana.

Labarai masu alaka