Ko akwai tsama tsakanin Salman, Aamir da Shahrukh Khan?

Shahrukh Khan, Salman Khan da Aamir Khan Hakkin mallakar hoto Desimartini
Image caption Shahrukh Khan da Salman Khan da Aamir Khan ba su da wata alaka ta jini amma suna kamanceceniya ta wasu bangarori

Shahrukh Khan da Salman Khan da kuma Aamir Khan manyan jarumai ne da suka yi suna a fina-finan Bollywood na Indiya, sannan kuma sun kafa tarihi a duniya baki daya saboda yadda fina-finansu suke tashe a kasashen duniya.

Ana ganin cewa sun kankane masana'antar shirya fina-finai ta Indiya, wato Bollywood.

Akwai abubuwa da dama da suke kamanceceniya misali, dukkaninsu an haifesu a shekara guda wato 1965, sai dai kuma kowanne da watan da aka haife shi.

Aamir Khan - An haife shi a ranar 14 ga watan Maris, 1965.

Shahrukh Khan - An haife shi 2 ga watan Nuwamba, 1965.

Salman Khan - An haife shi a ranar 27 ga watan Disamba, 1965.

Abu na biyu kuma da ya sa suke kamanceceniya shi ne kasancewar dukkansu musulmai, sannan kuma dukkansu suna amfani da sunan uba daya wato Khan.

Sai dai duk da wannan kamanceceniya, babu wata dangantaka ta jini a tsakaninsu 'The Three Khans' din.

Sannan kuma wata dangantakar da ke tsakaninsu ita ce yawancin fina-finansu duk na soyayya ne, in ban da dai-daiku.

Yadda suka fara fim

Aamir Khan

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Aamir Khan abi cika kwaramniya ba za a iya cewa shi dan ba ruwana ne

Aamir Khan ya fara fim ne tun yana karami dan shekara hudu, saboda kawunsa Nasir Hussain darakta ne, sai ya saka shi a fim din Yaadon ki Baraat.

Fim na farko da ya taka cikakkiyar rawa, ma'ana ya fito a cikakken jarumi shi ne, 'Qayamata se Qayamat Tak' wanda aka yi a shekarar 1988.

Tun daga nan kuma Aamir ya ci gaba da fitowa a fina-finai har zuwa yanzu.

Daga nan ne kuma a hankali shi ma ya fara shirya nasa fina-finan, inda ya kafa nasa kamfanin mai suna Aamir Khan Production a shekarar 1999.

Fim din 'Laagan' shi ne fim na farko da kamfanin ya fara shiryawa, kuma ya samu karbuwa sosai.

Yabo

Daga nan kuma sai ya ci gaba da shirya fina-finai, wanda kuma yawancinsu duk sun samu karbuwa

Daga cikin fina-finan da kamfanin Aamir Khan ya shirya, akwai 'Taare Zameen Par da Dangal' da kuma 'Secret Superstar.'

A tsawon shekaru fiye da 30 da Aamir ya yi a cikin masana'antar Bollywood, ya samu lambobin yabo da dama, ciki har da gwarzon jarumai a fina-finan Dil da Raja Hindustani.

Kazalika, fina-finan da kamfaninsa ya shirya ma sun samu lambobin yabo.

Shahrukh Khan

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An yi ittifakin cewa Shahrukh Khan ya fi sauran takwarorinsa 'ya'yan Khan arziki

Shahrukh Khan ya fara fim ne bayan da ya fito a cikin shirye-shiryen da ake nunawa a gidajen talbijin na Indiya wato Series.

Daga nan ne sai aka ga cewa ai zai iya yin fim ma, saboda yadda aka lura cewa yana taka rawa mai kyau a wadannan shirye-shiryen.

Fim na farko da Sharukh Khan ya fito a ciki, shi ne Deewana, wanda aka yi a shekarar 1992.

Shahrukh Khan ya fito a fina-finai da dama da suka yi tashe sosai kamar 'Kuch Kuch Hota Hai' da 'Baazigar' da 'Dilwale Dulhania Le Jayenge' da 'Dil To Pagal Hai' da kuma 'Kabhi Kushi Kabhi Gham.'

Shi ma ya bude kamfaninsa na shirya fina-finai mai suna Red Chillies Entertainment, wanda hadin gwiwa ne da matarsa Gauri Khan.

Daga cikin fina-finan da kamfaninsa ya shirya akwai 'Chalte-Chalte' da 'Main Hoon Na' da 'Om Shanti Om' da' Ra.One' da 'Chennai Express' da kuma 'Dilwale.'

Fina-finan da kamfaninsa ya shirya ma sun samu lambobin yabo.

Salman Khan

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salman Khan

Salman Khan ma ya fara fim ne 1989, da fim din 'Maine Pyar Kiya.'

Salman Khan ya yi fina-finai masu kyau da suka yi tashe, kamar 'Baaghi' da 'Hum Apke Hain Koun' da 'Hum Saath Saath Hain' da kuma 'Hum Dil De Chuke Sanam.'

Salman ya iya soyayya a fim, don kusan fina-finansa duk na soyayya ne.

Shi ma kamar sauran takwarorinsa 'yan gidan Khan, yana da nasa kamfanin na shirya fina-finan SKF, wato Salman Khan Film.

Daga cikin fina-finan da kamfaninsa ya shirya, akwai 'Bajrangi Bhaijaan' da 'Hero' da 'Tubelight' da kuma 'Race 3.'

Abubuwan da suka banbamta 'yan gidan Khan

Daukaka

Ta fuskar daukaka, dukkan jaruman su uku kowa na da tasa daukakar, to sai dai kuma idan aka zo batun tasiri, ana ganin cewa Shahrukh Khan ya fi sauran biyun tasiri.

Ta fiuskar yawan fina-finai kuwa, Salman Khan ne ya zarta sauran biyun, sai Shahrukh Khan sannan Aamir Khan.

A bangaren yawan magoya baya, Salman Khan ya fi sauran biyu yawan magoya baya a kasarsu wato Indiya.

Shi kuwa Shahrukh Khan, ya fi sauran biyun yawan magoya a Amurka da Afirka da kuma kasashen Turai, yayin da Aamir khan kuma ya fi sauran biyun yawan magoyan baya a China.

Masoya a kafafen sada zumunta

A bangaren kafafan sada zumunta kuwa, a shafin Facebook Salman Khan ne kan gaba wajen magoya baya, inda yake da mabiya miliyan 36.

Shahrukh Khan kuma yana da mabiya miliyan 28 a Faceboo, yayin da Aamir Khan ke da mabiya miliyan 15 shi ma a Facebook.

A Twitter kuwa shahrukh Khan ne ya fi dumbin mabiya inda mutum miliyan 35.3 ke bin sa.

Sai Salman Khan mai mutum miliyan 33.2, yayin da Aamir Khan ke da mabiya miliyan 23.3.

A shafin Instagram kuwa Salman Khan ne kan gaba da mabiya miliyan 16, Shahruk Khan yana da mabiya miliyan 12.7, sai Aamir Khan mai mabiya miliyan 841,000.

Masu gidan rana

A bangaren arziki kuwa Sharukh Khan duk ya fi su kudi, sai Salman Khan sannan kuma Aamir Khan.

Ko ya jituwa ta ke tsakaninsu?

Da fari dai akwai kyakkyawar jituwa tsakanin Salman Khan da Sharukh Khan, domin sun yi fina-finai fiye da uku tare, kamar 'Karan Arjun' da 'Hum Tum Hare Hai Sanam' da kuma 'Har Dil Jo Pyar Karega.'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Shahrukh Khan da Salma Khan

Amma a shekarar 2003 zuwa 2004, Salman Khan da Sharukh Khan sun taba samun sabani a lokacin da Shahrukh Khan ke shirya fim dinsa na Chalte-Chalte.

Da farko an shirya fim din a kan cewa Aishwarya Rai ce za ta kasance jarumar fim din har kuma an fara daukar fim din.

Ana cikin daukar fim din ne, sai Salman Khan da ya ke a lokacin suna soyayya da Aishwarya sai ya je wajen shirin fim din ya rinka daukarta suna fita, dole kuma komai ya tsaya.

Shahrukh ya yi masa magana a kan cewa yana janyo musu tsaiko, amma sai Salman ya ji haushi a kan don me zai ce masa haka.

Hakan ya sa har Sharukh Khan ya fusata ya ce a cire Aishwarya daga cikin fim din a maye gurbinta da Rani Mukherjee, da ya ke fim din na kamfaninsa ne.

Wannan matsalar haka ta yi ta ruruwa, har sai da kusan Bollywood ta rabu gida biyu, wato akwai 'yan banagaren Salman Khan da na Shahrukh Khan.

Da kyar dai bayan shafe shekara 8 zuwa 10, aka shirya su, kuma har yanzu suna ci gaba da abota.

To amma a bangaren Aamir Khan, za a iya cewa kusan shi dan ba-ruwana ne, sai dai kawai idan an hadu za a gaisa, amma daga bisani sun zo suna shiri da juna.

Aamir Khan dai bai taba fitowa fim tare da Shahrukh Khan ba, amma kuma sun yi fim tare da Salman Khan wato 'Andaz Apna Apna.'

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Salman Khan tare da Aamir Khan

Labarai masu alaka