'Yan gida daya biyar sun kai harin bam ofishin 'yan sanda a Indonesia

'Yan sanda a harabar ofishin bayan tashin bam din Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan sanda a harabar ofishin bayan tashin bam din

An samu fashewar bam a babban ofishin 'yan sanda na Surabaya, gari na biyu mafi girma a Indonesia.

Mutum biyar 'yan gida daya ne suka kai harin bam din bisa babura, in ji 'yan sanda.

Bam din ya tashi ne kwana guda bayan 'yan kunar bakin wake daga gida daya sun hallaka mutum 13 a wasu hare-hare da suka kai kan wasu majami'u a birnin, kuma kungiyar IS ta dauki alhakin kai hare-haren.

Wata 'yar shekara takwas ta tsira a harin na baya-bayan nan, in ji 'yan sanda.

Kasar Indonesiya ita ce kasar da ta fi yawan Musulmi a duniya.

Rahotanni sun nuna cewa wani dan kunar bakin wake ne da ke kan babur ya kai harin na baya-bayan nan.

Mai magana da yawun 'yan sanda a birnin ya ce al'amarin ya rutsa da jami'in dan sanda akalla daya.

Wani mutum Muhammad Wahibul Fadli da ke magana a wajen wata coci a Surabaya, ya ce akwai bukatar gwamnati ta kara zage damtse.

Labarai masu alaka