Koriya ta Arewa ta soke taron koli

Kim Jong-un and Donald Trump Hakkin mallakar hoto EPA/Getty

Koriya ta Arewa ta soke taron kolin da aka shirya yi tsakaninta da Koriya ta Kudu saboda ta ce wani atisayen soji da Amurka ke yi tare da Koriya ta Kudu a kusa da iyakar kasar wani shirin yaki ne.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa ya fitar da wata sanarwa wadda ta kuma gargadi Amurka cewa taron da aka shirya yi tsakanin shugaba Trump da shugaba Kim Jong-un na iya samun tangarda.

Tun da farko Koriyoyin biyu sun shirya tattaunawa a kan kyale iyalen da yakin Koriya ya raba.

Korea ta Arewa ce ma ta bada shawarar yin wannan taron, amma a yanzu an soke gudanar da shi gaba daya.

Kamfanin dillancin labarai na Koriya ta Arewa ya ce atasayen hadin gwuiwa da sojojin Amurka ke yi da na Koriya ta Kudu a matsayin dalilin soke taron. Koriya ta Arewa ta kuma ce atasayen wani mataki ne na tsokanar fada.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Amurka da Koriya ta Kudu sun sha cewa atasayen da suke yi na kariya ne kawai.

An dai fara gudanar da atasayen na sojoji mai suna Operation Max Thunder a ranar Jumma'a, kuma ya kunshi jiragen yaki guda 100 da suka hada da manyan jiragen yaki masu jigilar bama-bamai na B52 da kuma jiragen yaki na F15K.

Sanarwar ta kuma yi shaguben cewa ana iya soke taron da aka shirya gudanarwa tsakanin shugaba Kim Jong-un da shugaba Trump na Amurka, idan aak cigaba da atasayen.

Masu adawa da shirin kwance damarar kera makaman nukiliyar Koriya ta Arewa zasu kafa hujja da wannan halayyar da kasar ta nuna, cewa Koriya ta Arewa ba kasa ce da ya kamata a yarda da ita ba.

Labarai masu alaka