Musulmi sun fara azumin Ramadan

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Jawabin ganin wata daga bakin Sarkin Musulmi Sa'ad Abubakar
  • Latsa alamar lasifika da ke sama don sauraron jawabin ganin watan

Al'ummar Musulmi a Najeriya sun tashi da Azumi a ranar Alhamis bayan sanar da ganin jinjirin watan Ramadan a wasu sassan kasar.

Mai Alfarma Sarkin Musulmin Najeriya, Sa'ad Abubakar III, ne ya sanar da ganin jinjirin watan na Ramadan a Sakkwato da Borno da Zamfara da Bauchi da Gombe da Niger da kuma Fatakwal.

Kamar Najeriya, haka ma kasashen Musulmai da dama, da suka hada da Saudiyya za su fara azumin na watan Ramadan ne a ranar Alhamis.

Shugaba Muhammadu Buhari ya taya Musulmin kasar murnar shigowar watan azumin sannan ya yi kira da su mayar da hankali wurin bautar Allah da nuna soyayya ga bil'adama.

Sai dai kuma an soma azumin a wasu kasashen kamar Nijar tun a ranar Laraba.

Duk shekara, batun ganin watan Ramadan na janyo ce-ce-ku-ce a Najeriya sannan ana yawan samun sabanin fara azumi tsakanin Najeriya da makwabciyarta Nijar.

Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya Yakubu Dogara ya yi kira ga al'ummar Musulmin kasar da su yi amfani da wannan damar wurin addu'o'in neman zaman lafiya da hadin kan kasa.

A wata sanarwa da ya fitar, Mr Dogara ya ce kasancewar Azumi daya daga cikin shika-shikan Musulunci, "ina kira ga Musulmi da su yi amfani da albarkar da ke ciki wurin yin ibada da addu'o'in neman zaman lafiya a kasarmu".

Haka shi ma Shugaban Majalisar Dattawan kasar Bukola Saraki ya taya Musulmin kasar murna sannan ya nemi su yi addu'ar neman zaman lafiya da hadin kai a lokacin ibadunsu.

Azumin watan Ramadan na daya da cikin shika-shikan Musulunci. Ana kwashe kwanaki ashirin da tara ko talatin ana yin azumin.

Kuma Musulmi kan kaurace wa ci da sha da kuma saduwa da iyali daga fitowar alfijir har zuwa faduwar rana.

Ramadan wata ne mai alfarma da ake son Musulmi ya siffantu da bautar Allah da addu'o'i tare da neman gafara ga Mahalicci.

Labarai masu alaka