Ba Isa A Isa ne gwarzon jaruman Kannywood ba - AMMA

Kannywood Hakkin mallakar hoto Kannywood Instagram

Kwamitin da ya shirya bikin karrama mawaka da 'yan wasan kwaikwayo na Kannywood, wato AMMA Award na bana, ya ce Ado Ahmad Gidan Dabino ne ya kasance gwarzon jarumai na 2018, sabanin ikirarin da Isa A Isa ya yi a wata hira da BBC.

A makon da ya wuce ne aka yi birkin karrama ma'abota masana'antar Kannywood a birnin Katsina.

Shi dai Isa A Isa ya yi ikirarin cewa shi ne ya lashe kyautar gwarzon jaruman a wata hira da BBC a farkon makon nan.

Sai dai a tattaunawarsu da Ibrahim Isa, Shugaban kwamitin da ke shirya bikin, Bashir Yusuf ya yi karin haske, yana cewa watakila jarumin bai fahinci ainihin labar yabon da ya samu ba ne.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Bayanin AMMA kan jarumin jarumai

Anasa bangaren, Isa A Isa, wanda ya fito a fim din "Uwata ce," ya shaida wa BBC cewa karramawar ta zo ma shi da ba zata.

"Toh a gaskiya na tsinci kaina cikin wani farin ciki da ban ta ba zata zan samu a rayuwa ta ba saboda lokacin da na je wurin ance na fito a cikin jerin mutane bakwai da suka tsaya takarar kuma ban taba kawo wa ni zan samu ba", in ji shi.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Saurari hira da gwarzon Kannywood, Isa A Isa

Gwarazan AMMA na bana

 • Ado Ahmad Gidan Dabino shi ne gwarzon jarumi da fim din Juyin Sarauta.
 • Ya kayar da sauran mutum biyar da suka nemi wannan matsayi, wadanda suka hada da Lawal Ahmad da Sadik Sani Sadik, da Rabi'u Rikadawa da Shamsu Dan Iya da kuma Isa A Isa.
 • Ita kuma Halima Atete, ta zamo Jarumar Jarumai ta bangaren mata da fim din Karshen Tika Tiki.
 • Shi Isa A Isa an zabe shi a matsayin Fuskar Bikin Amma wato Face of AMMA Award.
 • Sannan Hafsat Idris ita ce Fuskar Bikin AMMA a mata.
Hakkin mallakar hoto Atete Instagram
Image caption Jarumar jarumai ta mata ta bana ita ce Halima Atete

Abubakar Waziri shi ne mataimakin gwarzon jarumi da fim din Dan Baiwa sai Maryam Ceta mataimakiyar jarumar jarumai mata da fin din Dr Halima.

Umar M Shareef ne ya lashe kyautar Jarumi mai tasowa da fim din Mansoor, yayin da Amar Umar ta lashe kyautar gwarzuwar jaruma mai tasowa da fim din Naja'atu.

Shi kuwa Sulaiman Bosho ya lashe kyautar wanda ya fi iya barkwanci ta Tunawa da Ibro, da fim din Dan Maigari.

Ahmad Ali Nuhu dan jarumi Ali Nuhu shi ne ya lashe kyautar jarumin jarumai a bangaren yara da fim din Dan Almajiri, yayin da mahaifinsa ya samu lambar yabo ta gwarzon mai shirya fina-finai da fim dinsa na Mansoor.

Sauran lambobin yabon da aka lashe:

Editan da ya fi kowa - Sanusi Dan Yaro da fim din "Uwata ce"

Mai daukar hoto - Nasiru S Dorayi da fim din Juyin Sarauta.

Hakkin mallakar hoto Hafsa Idris Instagram
Hakkin mallakar hoto Ali Nuhu
 • Fim din bayani da ya fi fice - Sulaiman Abubakar da shirinsa na Damarmakin Kasuwanci da Zuba Jari a Kano
 • Gagarabadan mai tsara dandali - Aliyu Shehu Yakassai da Abubakar Rashe da fim din Juyin Sarauta
 • Mafi kyawun hoto - Fim din Dan Baiwa
 • Fim din da ya fi gajarta mafi kyau - Gyara Kayanka
 • Kidan taushin da ya fi fice - Habibu Lafazi and Ibrahim Danko da fim din Juyin Sarauta
 • Sauti - Zahradeen Sound da fim din Dan Maigari
 • Kwalliya - Usaini 2pac da fim din Uwata ce
 • Zaben Sutura - Hamisu Lamido Iyantama da fim din Dan Baiwa
 • Tsara Labari na asali - Balaraba Ramat Yakubu da fim din Juyin Sarauta.

Labarai masu alaka