Ƙarnin jikin kaji na maganin sauro

Hakkin mallakar hoto Alamy

Masana kimiyya sun gano cewa sauron da ke dauke da kwayar cutar maleriya na kyamar irin karnin da jikin wasu dabbobi ko halittu ke yi, musamman ma kaji.

Masanan sun gudanar da bincike ne a kasar Habasha, inda suka fahinci cewa sauro ya gwamace ya sha jinin bil'adama maimakon jinin dabbobi, duk kuwa da cewa yana zukar jinin dabbobi irin su Shanu, da Awaki, da Tumaki, amma ko da wasa ba ya kusantar kaji.

Kazalika sauro na gudun wari ko karnin wani abu da aka cira daga jikin kaji, musamman gashin kajin.

Masanan sun ce watakila wannan binciken zai taimaka a yankunan da zazzabin cizon sauro ko maleriya ta zama annoba.

Labarai masu alaka