'Tattalin arzikin Nigeria zai kara taɓarɓarewa'

Hakkin mallakar hoto
Image caption Darajar kudin kasar na ci gaba da faduwa

Gwamnatin Najeriya ta ce akwai yiwuwar tattalin arzikin kasar ya fuskanci koma baya a karon farko cikin sama da shekara 20.

Ministan tsare-tsaren tattalin arzikin kasar Mr. Udoma Udo Udoma ne ya bayyana haka a wata hira da BBC a karshen taron Majalisar koli ta tattalin arzikin kasar da aka gudanar ranar Alhamis.

Sai dai ya ce gwamnati na daukar dukkan matakan da suka dace domin rage kaifin radadin da hakan zai yi ga 'yan kasar.

A farkon makon nan ne Asusun Bayar da lamuni na duniya ya rage hasashen ci gaba tattalin arzikin kasar na wannan shekara daga kashi 2.3 zuwa kashi 1.8.

Hakan ya faru ne saboda raguwar kudaden shigar da ake samu daga sayar da danyen mai da raguwar wutar lantarki da kuma rashin saka jari.

Labarai masu alaka