An yi garanbawul a majalisar dattijai

Image caption Sanata Saraki ya yi sauye-sauyen ne a ranar Alhamis

Shugaban Majalisar Dattijai ta Najeriya Bukola Saraki, ya yi sauye-sauye a shugabancin kwamitocin majalisar, inda ya bai wa masu adawa da shi manyan mukamai.

Majalisar ta sanar da sauye-sauyen ne a shafinta na Twitter ranar Alhamis, kafin ta gama zamanta na ranar inda ta fi hutu.

Wadanda suka samu sauyin shugabancin sun hada da Sanata Oluremi Tinubu, da Kabiru Marafa, wadanda ake ganin na gaba-gaba a sahun marasa jituwa da Mista Saraki.

An mayar da Sanata Marafa shugabancin kwamitin kula da bangaren man fetur daga na kula da kidayar jama'a.

Yayinda aka mayar da Tinubu zuwa kwamitin muhalli daga na kula da harkokin mata.

'Wasu kwamitocin'

  • Sanata Adamu Alairo shugaban kwamitin zirga-zirgar jiragen sama
  • Sanator Jibrin, shugaban kwamitin kula da manyan makarantu
  • Sanator Enyinnaya Abaribe, shugaba kwamitin wutar lantarki
  • Sanator Ovie Omo-Agege, shugaban kwamitin sufurin kasa

Sauye-sauyen shugabancin kwamitocin dai na daya daga cikin sharuddan da kungiyar hadin kan sanatoci ta sanya domin neman dawo da zaman lafiya a majalisar, wadda ake ta samun ce-ce-ku-ce a cikinta.

Mista Saraki ya ce sauye-sauyen na da alaka da wasu matakai da aka dauka a tarukan majalisar na sirri.

Labarai masu alaka