Zan hana baki shiga Amurka –– Trump

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Trump ne zai yi wa Republican takara

Dan takarar shugabancin Amurka a karkashin jam'iyyar Republican Donald Trump ya jaddada aniyarsa ta hana baki 'yan ci-rani shiga kasar da zarar ya zama shugaban kasa.

Ya ce bisa haka ne ma zai gina wata katanga tsakanin Amurka da Mexico.

Mr. Donald Trump ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabin amincewa da tsayar da shi takara da jam'iyyarsa ta yi.

Ya bayyana kan sa a matsayin murya ga Amurkawan da aka manta da su.

Ya kuma yi magori wasa kan-ka da kan-ka inda ya ce ta ko'ina ya zarta abokiyar hamayyar sa Hilary Clinton ta jam'iyyar Democrat, wacce ya bayyana a matsayin mai rashin sanin makama da ba ta dace da shugabanci ba.

Mr. Donald Trump ya kuma yi alkawarin kare Amurka daga abin da ya bayyana miyagun akidoji na kasashen waje.

Ya ce zai hada kai da duk kasashen da ke son ganin bayan kungiyar IS mai da'awar kafa daular musulunci.

Dan takarar ya ce zai kawo karshen tashe-tashen hankula da aikata laifuka a Amurka.