Rikicin siyasar Zamfara na kara kamari

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Takaddama ta soma ne bayan da majalisar ta nemi yin zama na musamman da gwamnan jihar

A Najeriya, bisa ga dukkan alamu rikicin siyasar daya barke a jihar Zamfara tsakanin gwamnan jihar da 'yan Majalisun dokokin jihar na kara za-fa-fa.

Yanzu haka shugabannin Majalisar dokokin jihar sun bayyana cewa ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen taka wa gwamna jihar birki kamar yadda doka ta ba su dama duk da tsare wasu 'yan Majalisun da jami'an tsaro suka yi.

A ranar litinin ne jami'an tsaron farin kaya suka kama kakakin Majalisar da Mataimakinsa da kuma wasu manyan jami'an Majalisar, lamarin da wasu suka yi zargin cewa da hannun gwamna jihar Abdul'aziz Yari.

Takaddamar dai ta soma ne bayan da majalisar ta nemi yin zama na musamman da gwamnan jihar domin tattauna abin da ta kira mawuyacin halin da jihar ta tsinci kanta a ciki.

A cewar 'yan majalisar amma sai gwamnan ya yi wa bukatar tasu mummunar fahimta cewa suna take-taken tsige shi.

Labarai masu alaka