'Yan gudun hijirar Syria na bukatar agaji

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan gudun hijirar na Syrai ba sa samun tallafi yadda ya kamata

Kungiyoyin bada agaji sun ce ana matukar bukatar kai kayayyakin tallafi ga 'yan gudun hijirar Syria fiye da 85,000 da ke kan iyakar kasar da Jordan.

Yanayin da ake ciki a yankin ya kara tabarbarewa ne tun bayan wani harin kunar bakin wake da aka kai kusa da wani tanti fiye da wata guda da ya wuce, inda aka kashe sojojin kasar Jordan su bakwai.

Bayan afkuwar hakan ne dai kasar Jordan ta ayyana kan iyakokin ta da ke Arewaci da kuma Kudanci a matsayin wasu wurare da sojoji ne kadai ke iya zuwa.

Kungiyar bada agaji ta Red Cross tare da kungiyar likitoci ta Medecines San Frontier sun roki Jordan ta ba su damar shiga yankunan da ke kan iyakokin.

Jordan na daya daga cikin kasashen da suka fi daukar 'yan gudun hijirar da rikicin Syria ya raba da gidajensu.

Labarai masu alaka