Ana zaman makoki a Afghanistan

Image caption Kimanin mutane 80 ne aka kashe a harin da aka kai cikin masu zanga-zanga

Al'ummar Afghanistan na zaman makoki a ranar Lahadi bayan wani harin kunar-bakin-wake da aka kai birnin Kabul ranar Asabar, wanda ya yi sanadin mutuwar kimanin mutum 80.

Fiye da mutum 230 ne kuma suka samu raunuka a harin da aka kai cikin masu zanga-zanga 'yan kabilar Hazara marasa rinjaye, wadanda galibin su 'yan Shi'a ne.

Kungiyar IS ta ce ita ce ta kai harin.

Shugaba Ashraf Ghani ya ce ya yi matukar bakin ciki da kai harin, inda ya sha alwashin daukar fansar mutanen da aka hallaka.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya bayyana harin a matsayin laifin yaki.

Wurin da akan kai harin bom din ya yi kaca-kaca, kuma an bukaci jama'a su taimaka wa wadanda lamarin ya shafa da jini.

Ma'aikatar cikin gida ta ce mutum uku ne suka je da niyyar kai harin, amma daya ne kawai ya yi nasara.

Ma'aikatar ta ce bom din daya daga mutanen ya ki tashi a lokacin da ya ke kokarin kai harin, daya maharin kuma jami'an tsaro sun harbe shi.

Akwai mayakan kungiyar ta IS a gabashin Afghanistan, sai dai a baya, ba su taba daukar alhakin kai hare-hare a babban birnin kasar ba.

Labarai masu alaka