Ruwan sama ya kashe mutane 70 a China

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Ambaliyar ruwa a Guangan

Ruwan sama mai karfin gaske ya yi sanadiyyar mutuwar mutane saba'in a China, da tilasta wa wasu miliyoyin mutane barin gidajensu.

Dubban gine gine kuma sun ruguje sakamakon ruwan saman.

Madatsar ruwa ta Three Gorges, ta cika makil, inda zurfin ruwan yakai mita dari da sittin da hudu.

Ruwan ya yi barna sosai a lardinan Hubei, da Liaoning da Hebei da kuma Henan.