Za a rusa rundunar tsaron musamman a Turkiya

Za a rusa rundunar tsaro ta musamman da ke fadar shugaban kasa a Turkiya yayin da Shugaba Recep Tayip Erdogan ke ci gaba da yin garambawul bayan yunkurin juyin mulkin soji da aka yi makon jiya da bai yi nasara ba.

Gwamnatin Turkiyar dai ta ce ba a bukatar rundunar tsaron ta musamman da ke da dakaru sama da dubu biyu da dari biyar a fadar shugaban kasa.

A jawabin da ya gabatar da aka watsa ta gidajen talbijin, Mr Erdogan ya ce duk wadanda ke da hannu a yunkurin juyin mulkin na da hakkin yi wa gwamnati da bangaren shari'a bayani kan hujjar su ta yin haka.

Ya kara da cewa kawo yanzu an kama fiye da mutum 13,000 da ake binciken su kan kulla makarkashiyar juyin mulkin da ba a yi nasara ba.

Daga cikin wadanda aka kama har da Halis Hanci wani na hannun daman Malamin addinin Musuluncin na dake zaune a Amurka Fethuallah Gulen wanda Mr Erdogan ya zarga da kitsa yunkurin juyin mulkin.

Labarai masu alaka