Damisa sun kashe wata mata a China

Hakkin mallakar hoto cctvchinanews
Image caption Mutumin da ke cikin motar bai samu rauni ba

Wasu damisa a gidan namun dajin Beijing da ke kasar China sun kashe wata mata sannan suka jikkata wata bayan matan biyu sun fito daga motar da suke ciki.

Kafofin watsa labaran kasar sun nuna wasu hotunan bidiyo kan yadda daya daga cikin matan ta fito daga mota, kuma nan take damisar suka kai mata farmaki sannan suka yi gaba da ita.

Sun kashe daya matar ne bayan ta fito domin taimakawa 'yar uwarta.

Wasu rahotanni sun ce matar ta farko ta fita daga motar ne bayan sun fara sa-in-sa da 'yar uwarta.

Sai dai wani mutum da ke tare da matan a cikin motar bai samu ko da kwarzane ba.

Ana barin mutanen da suka kai ziyara gidan namun dajin su tuka motarsu zuwa cikin gidan amma ban da wuraren da namun daji masu hatsari ke shakatawa.

Labarai masu alaka