Za a tsaurara dokar mallakar bindiga a Jamus

Image caption Manyan 'yan siyasa sun ce tsaurara dokar mallakar bindigogi za ta rage kisan kai na babu gaira babu dalili

Wasu manyan 'yan siyasar Jamus sun yi kira da a dauki kwararan matakai kafin a rika sayar wa mutane bindigogi, bayan harin da aka kai a Munich ranar Juma'a.

Mataimakin shugabar gwamnatin kasar Sigmar Gabriel ya ce ya kamata a dauki dukkan matakan da suka wajaba domin hana bai wa miyagun mutane damar mallakar muggan makamai.

Wani matashi David Sonboly, mai shekara 18, ya kashe mutum tara sannan ya kashe kansa a harbe-harben da ya yi a binrin na Munich.

An gano wata bindiga da harsasai fiye da 300 a gidansa.

Minista a ma'aikatar cikin gidan kasar Thomas de Maiziere, wanda ya kai ziyara a wurin da aka yi harbe-harben, ya ce yana shirin yin garambawul ga dokokin mallakar bindigogi.

Labarai masu alaka