Rio: Ba duka 'yan wasan Rasha aka dakatar ba

Kwamitin shirya wasannin Olympic na duniya ya ce ba zai dakatar da dukkan 'yan wasan tawagar Rasha daga shiga gasar wasannin da za a yi a birnin Rio ba.

Kwamitin ya dauki wannan mataki ne duk da cewa sakamakon wani bincike ya nuna gwamnatin Rasha ta tafiyar da wani shirin amfani da kwayoyi masu kara kuzarin 'yan wasan har na shekara hudu.

Kazalika, kwamitin ya ce wajibi ne suma hukumomin shirya wasanni na kasa da kasa su yi kyakkyawan nazarin sakamakon gwajin amfani da kwayoyi masu kara kuzari a kan kowanne dan wasa.

Duk wani dan wasa daga Rasha da aka amince da shi, zai kuma fuskanci wani karin gwaji mai tsanani.

Ba za a bar kowanne dan wasa daga Rashan da aka hukunta shi a baya sakamakon amfani da kwayoyin, ya shiga wasanni na Rio ba, da za a fara kasa da makonni biyu masu zuwa.

A ranar Alhamis ne ya tabbata cewa Rasha ba ta yi nasara ba a daukaka karar da ta yi a kotun kararrakin wasanni, kan hana wasu 'yan wasan kasarta shiga wasannin da za a yi a Rio.

Labarai masu alaka