Nigeria: An kama mai yaɗa jita-jitar juyin mulki

Hakkin mallakar hoto EPA

Hukumar tsaro ta farin-kaya a Najeriya, DSS ta ce ta kama wani fitaccen dan kungiyar yankin Naija Delta wanda take zargi da yada jitar-jitar cewa suna shirin yi wa gwamnatin kasar juyin mulki.

DSS ta ce ta kama Jones Abiri wanda ake yi wa lakabi da Janar Akotebe Darikoro, shugaban kungiyar Joint Revolutionary Council of the Joint Niger Delta Liberation Force ne ranar 21 ga watan jiya a Yenagoa, babban birnin jihar Bayelsa.

Hukumar ta ce mutumin ne ya rika bayyana cewa suna hada baki da wasu jami'an tsaron kasar domin kifar da gwamnatin Muhammadu Buhari.

A cewar hukumar, Darikoro na daya daga cikin mutanen da suke kai hare-hare a kan bututan man fetur na yankin, lamarin da ya sa kasar ta yi asarar biliyoyin kudi sakamakon dakatar da hakar man.

DSS tana kuma zarginsa da hannu a kai hare-hare kan bututan man kamfanin Agip Oil da ke Ogboinbiri, da na Shell Petroleum Development Company a Brass Creek, duk dai a jihar ta Bayelsa.

Labarai masu alaka