Kotu ta wanke Salman Khan a shari'ar farauta

Image caption Salman Khan na daga cikin fitattun jaruman fim na India, inda a yanzu ya shiga sama da fim 80

Wata kotu a India ta wanke fitaccen jarumin fina-finan kasar Salman Khan, a shari'ar da ake zarginsa da laifin farautar dabbobin da ke fuskantar gushewa a doron kasa, shekara 20 da ta wuce.

An tuhumi jarumin da wasu mutane bakwai da kisan dabbobin daji da suka hada da gada da mariri a arewacin jihar Rajasthan a shekarar 1998.

A watan da ya wuce ya jawo ka-ce-na-ce a lokacin da ya sheda wa manema labarai a game da fim dinsa na baya-bayan nan cewa aikin fim din yana da wahala matuka domin ya sa yana jin kamar an yi masa fyade kamar mace.

Jarumin ya kalubalanci hukuncin wata karamar kotu ne da ta yanke masa hukuncin shekara daya da kuma shekara biyar a gidan yari a kan laifukan biyu na farauta.

Ainahin shari'ar dai al'ummar yankin Bishnoi ne wadanda suke bauta wa bakin mariri suka shigar da karar.

A shekarar da ta wuce kotu ta wanke Salman Khan bayan tuhumarsa da laifin take wani mutum maras galihu da ke kwana a titi a wani hadarin mota.

Gwamnati ta daukaka kara a kan wanke jarumin a kotun koli.