'Yan Shi'a na neman agaji kan El-Zazzaky

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kungiyar ta ce lafiyar shugaban nata na kara tabarbarewa

Kungiyar 'Yan uwa musulmi ko Islamic Movement ta mabiya mazhabar Shi'a a Najeriya ta nuna damuwa a bisa lafiyar shugabanta, Sheikh Ibrahim El-Zazzaky, wanda ke hannun jami'an tsaro.

A wani taron manema labarai a Kaduna, wasu shugabannin kungiyar sun ce a bisa bayanan da suka samu lafiyar shugaban nasu na ci gaba da tabarbarewa a yayin da ake ci gaba da tsare shi .

A kan haka ne suke bukatar al'umma da duk wasu da suka ce masu lura da tunani ne a cikin jama'a da su sanya baki a sake shi don nema masa magani.

A cewar farfesa Abdullahi Danladi wanda ya yi magana a madadin sauran shugabannin ya ce, iyalan El-Zazzakyn sun shaida musu cewa, sannu a hankali yana makancewa, kuma wani bangare na jikinsa na shanyewa.

Kakakin ya ce matar El-Zazzakyn wadda ita ma tana tare da malamin a tsare, tana cikin wani hali domin akwai harsashi a cikin jikinta a kusa da lakarta, abin da ke bukatar a je waje da ita domin a yi mata aiki.

Kungiyar ta kuma ce akwai 'yan'yanta da yawa da jami'an tsaro suke tsare da su a gidan kurkuku, kuma suna kira da su ma a sako su.

Tun a watan Disambar shekarar da ta wuce ne jami'an tsaron Najeriya ke rike da Sheikh El-Zazzaky bayan wata arangama tsakanin yan kungiyar da Sojoji a Zaria.

Arangamar ta haddasa jikkata da asarar rayuka da dama na 'yan kungiyar ta Shi'a.

Labarai masu alaka