Bam ya tashi a birnin Damascus

Harin bam a nirnin Damascus Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin da akeyi a Syria tsakanin dakarun gwamnati da 'yan tawaye, ya daidaita kusan rabin kasar.

Kafar yada labaran Syria ta ce wani bam da aka dasa a cikin mota a unguwar da gine-gine gwamnati ke da yawa, ya tashi a babban birnin kasar Damascus. Harin ya kuma shafi gidajen wasu mayakan sa kai 'yan kasar Iran.

Yayin da ake ci gaba da gwabza fada babu kakkautawa a ciki da wajen birnin Aleppo.

A yau ne kuma ake sa ran manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya da Amurka da kuma Rasha za su tattaunawa a Geneva, dan lalubo hanyar da za a sabuwar yarjejeniyar zaman lafiya a Syria za ta fara aiki da kuma dorewa.

Kididdiga ta nuna fararen hula su rikicin na Syria ya shafa, cikin su kuma mata da kananan yara da tsofoffi ne suka fi shan wahala.

Labarai masu alaka