An kama mutumin da ke lalata da 'yan mata

Image caption Mista Aniva da ake kira Kura ya ce ya kwanta da mata fiye da 100

Hukumomi a kasar Malawi sun kama mutumin da ake biya a wani yanki na kasar domin ya rika saduwa da 'yan mata, wanda ya yi hira da BBC yana cewa ana daukar hayarsa ne don ya tsarkake yaran.

Shugaba Peter Mutharika ne ya bayar da umarnin kama Eric Aniva da ake kira ''Kura''.

Daraktan yada labarai na fadar shugaban kasa Bright Molande, ya shaida wa BBC cewa za a gurfanar da Mista Aniva a gaban kuliya saboda keta haddin yara da yake yi.

Ya kuma ce shugaban kasa ya kadu sosai da jin irin abubuwan da ke faruwa da sunan al'ada a labarin da BBC ta wallafa, inda ya kudiri aniyar wargaza wannan al'ada.

A cikin labarin, Mista Aniva, ya ce ya yi jima'i da mata fiye da 100, kuma yana dauke da kwayar cutar HIV.

Dattijai ne suke goyon bayan wannan al'ada ta yin jima'i da 'yan matan da suka fara tasawa da sunan ''tsarkakewa'' a Kudancin Malawi, amma gwamnati ta dade tana adawa da al'adar.

A lokacin da BBC ta yi labarin a makon da ya gabata, mutane da dama daga sassa daban-daban na duniya sun yi Allah-wa-dai da al'adar.

Labarai masu alaka