'Yan majalisa mutanen banza ne — Obasanjo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ba wannan ne karon farko da Obasanjo ya caccaki 'yan majalisar ba

Tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo ya ce yawancin 'yan majalisar dokokin tarayya "mutanen banza" ne.

Obasanjo ya bayyana haka ne a hirarsa da 'yan jarida a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja, babban birnin kasar.

Tsohon shugaban kasar ya ce, kamar yadda ya sha nanatawa a baya, 'yan majalisar dokokin tarayya ba su da martaba.

'Yan jarida sun tambayi tsohon shugaban kasar ne kan yadda za a shawo kan rikicin da ya barke tsakanin wani dan majalisar wakilai da wasu shugabannin majalisar kan cuwa-cuwa a kasafin kudin 2016, inda ya ce "maimakon a shawo kan wannan rikici, ya kamata a rikar zabar maza da matan da suke da martaba."

Obasanjo ya ce, "Ya kamata shugaban kasa ya rika sa ido sosai kan irin mutanen da za a zaba domin zama 'yan majalisa."

A baya ma dai tsohon shugaban na Najeriya ya taba zargin cewa 'yan majalisar miyagun mutane ne da ba su da kishin kasa.

Sai dai 'yan majalisar sun ce kura ba za ta cewa kare maye ba.

Labarai masu alaka