Jirgi mai amfani da rana ya kammala zagaya duniya

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Matukan biyu sun rungume juna cikin farin ciki bayan kammala zagayen

Jirgi mai amfani da hasken rana na Impulse ya kammala zagaya duniya bayan da ya sauka a kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Bertrand Piccard shi ne ya tuka jirgin a sawu na karshe daga birnin Alkahira zuwa kasar Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sun rinka yin karba-karba ne da Andre Borschberg, dan kasar Switzerland a kokarinsu na bunkasa amfani da makamashin da ake sabuntawa.

Wannan shi ya kawo karshen zagayen da jirgin ya fara daga birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa a ranar 9 ga watan Maris na shekarar 2015.

A zagayen duniyar da jirgin ya yi, ya yi tafiyar kilomita 42,000 inda ya shiga nahiyoyi hudu da manyan koguna biyu da kuma tekuna biyu.

Tafiya mafi tsawo da jirgin ya yi a zagayen ita ce ta kilomita 8,924 daga Nagoya na kasar Japan zuwa Hawaii a Amurka, inda ya shafe sa'o'i 118, wanda hakan ya sa matukin Mista Borschberg ya zama na farko da ya yi tafiya mai tsawo irin haka a duniya.

Mista Piccard da Mista Borschberg sun shafe gomman shekaru suna aiki kan jirgin.

Yadda tafiyar jirgin ta kasance

Sawun farko: 9 ga watan Maris daga birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa zuwa birnin Muscat na Oman - kilomita 772 cikin sa'o'i 13 da minti daya

Sawu na biyu: 10 ga watan Maris. Daga birnin Muscat na Oman zuwa birnin Ahmedabad na Indiya - kilomita 1,170 cikin sa'o'i 15 da minti 20

Sawu na uku: 18 ga watan Maris. Daga Ahmedabad na Indiya zuwa birnin Varanasi a Indiya - kilomita 1,170 cikin sa'o'i 13 da minti 15

Sawu na hudu: 18 ga watan Maris. Daga Varanasi na India zuwa Mandalay na kasar Myanmar - kilomita1,536 cikin 13 da minti 29

Sawu na biyar: 29 ga watan Maris. Daga Mandalay na Myanmar zuwa birnin Chongqing na China - Kilomita 1,636 cikin sa'o'i 20 da minti 29

Sawu na shida: 21 ga Afrilu. Daga Chongqing na China zuwa birnin Nanjing na China - kilomita 1,384 cikin sa'o'i 17 da minti 22

Sawu na bakwai: 30 ga watan Mayu. Daga Nanjing na China zuwa birnin Nagoya na Japan - kilomita 2,942 cikin kwana daya da sa'o'i 20 da minti tara

Hakkin mallakar hoto solar plane

Sawu na takwas: 28 ga watan Yuni. Daga Nagoya na Japan zuwa birnin Kalaeloa, Hawaii na Amurka - kilomita 8,924 cikin kwana hudu da sa'o'i 21 da minti 52

Sawu na tara: 21 ga Afrilu. Daga Kalaeloa, Hawaii na Amurka zuwa birnin California na Amurkar - kilomita 4,523 cikin kwana biyu da sa'o'i 17 da minti 29

Sawu na 10: 2 ga watan Mayu. Daga Mountain View a California Amurka zuwa Phoenix a Arizona na Amurka - kilomita 1,199 cikin sa'o'i 15 da minti 52

Sawu 11: 12 ga watan Mayu. Daga Phoenix, Arizona a Amurka zuwa Tulsa, Oklahoma a Amurka - kilomita 1,570 cikin sa'o'i 18 da minti 10

Sawu na 12: 21 ga watan Mayu. Daga Tulsa, Oklahoma na Amurka zuwa Dayton, Ohio na Amurka - kilomita 1,113 cikin sa'o'i 16 da minti 34

Sawu na 13: 25 ga watan Mayu. Daga Dayton, Ohio na Amurka zuwa Lehigh Valley, Pennsylvania a Amurka - kilomita 1,044 da sa'o'i 16 da minti 47

Sawu na 14: 11 ga Yuni. Daga Lehigh Valley, Pennsylvania na Amurka zuwa birnin New York na Amurka - kilomita 230 cikin sa'o'i hudu da minti 41

Sawu na 15: 20 ga watan Yuni. Daga birnin New York na Amurka zuwa birnin Seville na Spaniya - kilomita 6,765 cikin kwana biyu da sa'o'i 23 da minti 8

Sawu na 16: 11 ga Yuli. Daga Seville na Spaniya zuwa birnin Alkahira na Masar - kilomita 3,745 cikin kwana biyu da minti 50

Sawu na 17 kuma na karshe: 23 ga Yuli. Daga Alkahira na Masar zuwa birnin Abu Dhabi na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa - kilomita 2,694 cikin kwana biyu da minti 47