An kashe mutum 10 a Somalia

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Al-Shabaab ta dauki nauyin kai hare-haren

'Yan sanda sun ce akalla mutum goma ne suka mutu a wasu hare-haren bama-bamai biyu a kusa da babbar kofar shiga filin jirgin saman Mogadishu, babban birnin Somaila.

Hayaki ya turnike sararin samaniyar birnin, inda a can ne sansanin dakarun kiyaye zaman lafiya na kungiyar Tarayyar Afirka yake.

'Yan jarida sun ce 'yan kunar bakin-wake ne suka tashi bam na farko a kusa da wani wurin binciken abubuwan hawa.

An yi amannar cewa cikin mutanen da suka mutu har da jami'an tsaron da ke sanya ido a wurin binciken abubuwan hawan.

Kungiyar al-Shabab, wacce ke da alaka da kungiyar al-Qaeda, ta ce ita ce ta kai hare-haren a yunkurinta na tumbuke gwamnatin kasar, wacce majalisar dinkin duniya ke mara wa baya.

Labarai masu alaka