Ba hannunmu a juyin mulkin Turkiyya — UBA

Hakkin mallakar hoto
Image caption A ranar 15 ga watan Yuli ne aka yi yunkurin juyin mulki a Turkiyya, amma bai yi nasara ba

Bankin UBA a Najeriya ya yi watsi da zargin da aka yi cewa yana da hannu a yunkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiyya a makon da ya gabata.

Hakan ya biyo bayan zargin da wata jarida ta kasar Turkiyya mai goyon bayan gwamnati ta yi ne cewa an yi amfani da bankin wajen aika wa wadanda suka shirya juyin mulkin kudade.

A wata sanarwa da ya fitar, bankin UBA ya ce yana sane da jita-jitar da ake yadawa a kansa, don haka ne ya yanke shawarar wanke kansa.

''Babban burinmu shi ne mu gina Afirka tare da ciyar da ita gaba ta hanyar ingantacciyar mu'amalar kudade,'' a cewar sanarwar.

A ranar 15 ga watan Yuli ne aka yi yunkurin juyin mulki a Turkiyya, amma bai yi nasara ba.

Labarai masu alaka