Ba zan daina maraba da 'yan hijira ba — Merkel

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Hare-hare biyu 'yan gudun hijira suka kai Jamus a baya-bayan nan

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta ce ba za ta watsar da shirinta na karbar bakuncin 'yan gudun hijira ba, duk kuwa da hare-haren bayan-bayan nan da wasu masu neman mafaka a kasar suka kai.

Misis Merkel ta ce a bayyane yake cewa mutanen biyu, wadanda suka shigo cikin Jamus a matsayin 'yan gudun hijira sun kai hare-haren ne da sunan kungiyar IS, kuma tamkar sun watsa wa kasar kasa a ido ne .

Ta ce za ta yi bakin kokarinta don ganin ta tabbatar da tsaro.

Misis Merkel ta kara da cewa, '''Yan ta'adda suna son su ga mun kauce daga hanya kan abin da ke da muhimaci a wurinmu. Suna son su ga sun kawo tangarda kan hadin kai da ke tsakaninmu da kuma zaman lafiya.''

Sai dai shugabar ta kuma ce ba za ta bar 'yan ta'adda su kawo cikas ga al'adar yin maraba da baki ta Jamus ba.

Labarai masu alaka