Akwai barazanar yunwa a Nigeria

Babban jami'in kula da ayyukan jin kai na majalisar dinkin duniya Stephen O'Brien ya yi kashedin cewa bala'in yunwa na iya aukawa wasu sassan Nigeria da kuma yankin tafkin Chadi.

Majalisar Dinkin Duniyar ta kuma yi kiran a gaggauta daukar matakai wajen shawo kan matsalolin da 'yan gudun hijira ke fuskanta a yankin.

Kusan mutane miliyan uku ne dai rikicin Boko Haram ya raba da muhallinsu a Najeriya da Kamaru da Chadi da kuma Nijar.

Jibrin Santumari shi ne shugaban kwamitin kula da hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa na majalisar wakilan kasar, Isa Sanusi ya tambaye shi ko me zai ce dangane da matsalar yunwa da ake fama da ita a yankin Arewa maso Gabas:

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Labarai masu alaka