Zaki ya tsere daga gidan namun daji

Image caption Wannan ne karo na uku da zaki ke tserewa daga gidan namun daji a wannan shekarar

Wani zaki ya tsere daga gidan namun dajin Nairobi, babban birnin kasar Kenya.

Hukumar da ke kula da gidan namun dajin ta ce zakin yana gararamba a yankin Karen da ke birnin na Nairobi.

Ta kara da cewa tana kokarin hilatar zakin domin sake kai shi gidan namun dajin.

Akwai dai wata babbar hanya tsakanin gidan namun dajin da kuma cikin birnin.

Wannan ne karo na uku da zaki ke tserewa daga gidan namun daji a kasar ta Kenya.