Giwa ta kashe wata yarinya da dutse

Hakkin mallakar hoto
Image caption Masana halayyar dabbobi sun ce ba kasafai giwa ke nuna irin wannan dabi'a

Wata yarinya 'yar shekara bakwai ta rasu bayan da wata giwa ta jefe ta da dutse a gidan namun daji na birnin Rabat da ke kasar Moroko.

Giwar ta jefa dutsen ne daga kejinta inda ya tsallake shingen da aka sa a tsakanin wajen da dabbobin suke da kuma inda mutane ke tsayawa, har ya samu yarinyar.

A take aka garzaya da yarinyar asibiti, amma bayan sa'o'i kadan sai ta ce ga garinku.

Wata sanarwa da hukumar gidan namun dajin ta fitar, ta ce an kewaye wajen da dabbobin suke kamar yadda tsarin kasashen duniya ya tanada.

Sanarwar ta kuma ce, ''Irin wannan abu bai cika faruwa ba sai bisa tsautsayi.''

Ta kara da bayar da misalan irin wadannan abubuwa da suka faru a wasu kasashen kamar Amurka, inda a watan Yuni wata katuwar kada ta kashe yaro dan shekara biyu a wajen shakatawa na Walt Disney World.

A watan Mayu ma wani yaro ya fada kejin wani goggon biri a Cincinnati, har sai da ma'aikatan wajen suka kashe birin don a tserar da yaron.

Masana halayyar dabbobi dai sun ce ba kasafai giwaye ke jifa da duwatsu ko itace ba, irin haka na faruwa ne a lokacin da suka fusata.