Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Rikicin majalisar wakilai ya yi kamari

A Nigeria, tsohon shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilan Nigeria, Abdulmumini Jibrin ya ce yana nan kan bakansa dangane da zargin aikata ba daidai ba da ya yi wa shugabannin majalisar wakilan.

Wata sanarwar da ya fitar ta ce Hon. Abdulmumini Jibrin ba zai nemi gafara ba dangane da zarge-zargen da ya yi wa shugabannin majalisar.

Tuni dai kakakin majalisar wakilan Yakubu Dogara ya bukaci Abdulmumini Jibrin ya janye zargin da ya yi masa ko ya dauki matakin shari'a.

Amma Hon. Abdulmumini Jibrin ya ce ba gudu ba ja da baya.

Mun dai yi kokarin samunsa domin jin ta bakinsa, amma ba mu same shi ba.

Ga rahoton da Isa Sanusi ya hada mana:

Labarai masu alaka