'Boko Haram na cin zarafin mutane'

Majalisar Dinkin Duniya
Image caption Majalisar Dinkin Duniyar ta ce fiye da mutane miliyan 10 ne suka rasa muhallansu a yankin tafkin Chadi.

Majalisar Dinkin Duniya ta zargi mayakan kungiyar Boko Haram a Najeriya da gallaza wa mutane da kisan wadanda ba su ji ba ba su gani ba a kasar.

Jami'in da ke kula da ayyukan jinkai na Majalisar, Stephen O'Brien, ya ce rikicin Boko Haram ya tilasta wa dubban mutane barin muhallansu, yayin da miliyoyin mutane ke tsananin bukatar taimako.

Kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna fiye da mutum miliyan 10 da ke yankin Tafkin Chadi suka yi hijira cikin yankunan Najeriya da Jamhuriyar Nijar, da Kamaru da ita kanta Chadin, kuma suna bukatar taimako.

Halin da Boko Haram ta jefa yara

Boko Haram ta tilasta wa yara da dama yi mata aiki

50

Yawan yaran da suka kai harin kunar-bakin-wake cikin wata shida

  • 250,000 Yaran da ke fama da tamowa a Borno

  • 9m Mutanen da ke bukatar agajin gaggawa a yankin tafkin Chadi

AFP

Mutanen sun tsere wa tashin hankali da kashe-kashen 'yan Boko Haram a kauyuka da garuruwan arewa-maso-gabashin Najeriya da kasashe makwabta.

Labarai masu alaka