Shugaban Amazon ya shiga sawun manyan attajirai

Jeff Bezos Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaban Amazon Jeff Bezos

Mujallar Forbes ta sanya shugaban Amazon, Jeff Bezos, a matsayin attariji na uku a duniya sakamakon karuwar da kamfanin ya samu a kudin shiga da habaka a hannayen jarinsa.

Mista Bezos ya mallaki kashi 18 cikin 100 na hannayen jarin kamfanin.

Mujallar Forbes ta yi kiyasin cewa dukiyarsa ta kai dala biliyan 65.

Kudin da Amazon ya samu ya wuce adadin da masu sharhi suka kiyasta zai samu, inda ya karu daga kashi 31 cikin 100 a bara zuwa dala biliyan 30 a cikin wata hudu da suka gabata.

Ribar da kamfani mafi girma kan kasuwanci ta hanyar internet ya samu ta kai dala miliyan 85, idan aka kwatanta da ribar dala miliyan 92 da ya samu a 2015.

Mujallar Forbes ta bayyana cewa shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates da aka kiyasta cewa dukiyarsa ta kai dala biliyan 78 da shugaban kamfanin Zara Amancio Ortega da shi ma aka kiyasta cewa dukiyarsa ta kai dala 73 su ne suke gaban Mista Bezos a duniya.