Najeriya za ta binciki makarantun Turkiyya

Hakkin mallakar hoto Nigeria Senate
Image caption Jakadan Turkiya ya bukaci hukumomin Najeriya da su rufe makarantun da ke da alaka da Fethullah Gulen

Majalisar dattijan Najeriya ta ce akwai bukatar a yi bincike don gano gaskiyar zargin cewa makarantun da ke da alaka da Fethullah Gulen a Najeriay na da hannu a yunkurin juyin mulkin da aka yi a Turkiyya.

Jakadan Turkiyya a Najeriya Mr Hakan Cakil ne ya yi wannan zargi lokacin da 'yan kwamitin kula da harkokin kasashen waje na Majalisar suka kai masa ziyara a ofishin sa.

Jakadan ya kuma bukaci hukumomin Najeriya su rufe makarantun.

Sai dai Sanata Shehu Sani, mataimakin shugaban kwamitin ya shaida wa BBC cewa za a gudanar da bincike kuma matukar zargin da jakadan ya yi ya tabbata, gwamnatin Najeriya za ta dauki matakai.

Tun bayan yunkurin juyin mulkin a Turkiya dai gwamnatin kasar ta rufe daruruwan makarantu a kasar, musamman masu alaka da mlamin addinin nan Fethullah Gulen, wanda aka zarga cewa ya na da hannu a juyin mulkin.

Labarai masu alaka